Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Matashi Bakar Fatar Amurka Abun Takaici ne


Zanga-zangar a Ferguson, Missouri ga 17 Augusta 2014.
Zanga-zangar a Ferguson, Missouri ga 17 Augusta 2014.

Rev. Al Sharpton ya furta haka ne a lokacin da yake jawabi a wani gangamin da aka yi a garin Ferguson.

Madugun kare hakkokin bakaken fatar kasar Amurka, Rev. Al Sharpton ya bayyana cewa harbin kisan da wani dan sanda bature ya yiwa wani matashi bakar fata da ba ya dauke da makami, wani abun takaici ne.

Sharpton ya furta haka ne a lokacin da yake jawabi a wani gangamin da aka yi a garin Ferguson, inda munanan zanga-zanga da kwasar ganima suka barke bayan harbin da ya kashe Michael Brown dan shekaru 18 a ranar 8 ga watan ga agusta.

Da safiyar jiya lahadi sakataren shari'ar Amurka Eric Holder ya ce wani kwararren likitan gwamnatin tarayya mai binciken sanadin mutuwa zai sake duba gawar Brown kamar yadda iyayen shi suka bukata kuma saboda irin sarkakkiyar dake tattare da lamarin.

Haka nan kuma gwamnan jahar Missouri Jay Nixon ya ce za a ci gaba da kafa dokar hana fita da ba iyaka, saboda fito na fiton da ake yi yawanci da daddare tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga.

Ko dayake shugaba Barack Obama ya na hutu a tsibirin Martha's Vineyard a arewa maso gabashin jahar Massachussetts, amma hakan bai hana yi m shi bayani akai-akai ba game da zanga-zangar dake faruwa a garin Ferguson.

Da safiyar jiya lahadi, an kama mutane bakwai a garin na Ferguson a daidai lokacin da 'yan sanda suka yi amfani da hayaki gami da barkonon tsohuwa a kokarin da suke yi na tabbatar dokar hana fitar. A cewar hukumomi wani mutum guda yayi mummunan rauni sanadiyar wani harbin da ya faru a wajejen, amma ba shi da alaka da zanga-zangar dake gudana.

XS
SM
MD
LG