Wata arangama da ta hada ‘yan acaba masu dauko man petur daga Najeriya, da jami'an douane ko kwastam tayi sanadiyar rasuwar wani matashi dan acaba a garin Magaria, abinda ya harzuka ‘yan uwan shi ‘yan acaba suka far ma runfar jami'an suka kona ta da wasu kayayyaki, a cewar Mamman Marji, daraktan wani gidan rediyo dake garin Magaria.
Bayan haka, matasan suka iso garin Magaria inda suka fara kone-konen tayoyi, amma mataimakin shugaban gundumar Magaria Hasan Bubakar, da mai Martaba sarkin Magaria suka taresu, tare da ba su hakuri.
Bayan an yiwa mamacin jana'iza mahukuntan sun zauna da matasan har da iyaye da ‘yan uwan yaron suka ba su hakuri, sun kuma ba su dama su zayyana dukan matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya. Bayan sun saurare su, sun kuma yi alkawarin duba matsalolin tare da gano bakin zaren, duba da yadda wannan lamari yayi sanadiyar asarar rai.
A nasu bangaren, matasan sun gamsu ainun da yadda hukumomin na Magaria suka tunkari lamarin, da yadda suka kwantar musu da hankali, har suka yi alkawarin cewa za a biwa matashin da ya rasa ransa hakki, abinda ya dadadawa matasan rai.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana
-
Maris 20, 2023
Ranar Farin Ciki Ta Duniya
Facebook Forum