Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Menene Dalilin Ziyarar Kwanaki Hudu Da Shugaba Buhari Zai Kai Ingila?


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai tafi Ingila na tsawon kwanaki hudu wadda take da nasaba da duba lafiyarsa.

Ziyarar ta samo asali ne sanadiyar yada zangon da yayi a Ingila kan hanyar komawarsa Najeriya daga ziyarar da ya kawo nan Amurka. Lokacin ne likitocinsa suka umurceshi ya koma domin su duba lafiyarsa.

Kakakin fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu, shi ya aikawa manema labaru rubutaciyar sanarwa inda ya tabbatar cewa a yau Talata shugaban zai yi wannan balaguron.

Bayan ya koma gida Najeriya, shugaban zai kai ziyara jihar Jigawa makon gobe, wadda tun farko aka daga ta saboda da tarukan jam’iyyar APC da ake yi na fitar da shugabanninkananan hukumomi da jihohi.

Jiya Litinin shugaban ya gana da shugabannin majalisun tarayya, wato shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da na majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Shugaba Buhari ya gana da shugabannin majalisun ne domin ya yi masu bayani akan ziyararsa zuwa Amurka. Su ma shugabannin majalisun sun gabatar da koke-kokensu akan abun da suka kira cin mutuncin da ake yiwa ‘yan majalisa, musamman abun da ya faru a lokacin da aka yiwa majalisar dattawa karan tsaye yayinda aka ce Sanata Omogege aka ce ya shiga majalisar da wasu ‘yan banga da suka sace sandar majalisar. Haka ma aka yiwa Sanata Dino Melaye kamun kazar kuku lamarin da ‘yan majalisar ke ganin an yiwa tsarin Dimokradiya ne karan tsaye ne.

Bayan bayanan da shugabannin majalisun suka gabatar masa, shugaba Buhari ya yi juyayin abun da ya faru kuma ya bada tabbacin za’a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da cewa an yi adalci akan lamarin.

Shi ko shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara cewa ya yi abun da ‘yan sanda ke yi abu ne da aka yi lokacin jahiliya ba na lokacin Dimokradiya ba saboda haka kowane rukunin gwamnati ya yi anfani da dokokin kasa akan ladaftar da wadanda ake zargi da wani laifi ba tare da yiwa mutum wulakanci ko kaskanci ba.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG