Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kobe Bryant Ya Rasu a Hatsarin Jirgin Sama


Masu sha’awar kwallon Kwando a fadin duniya na alhini da jimamin mutuwar tsohon dan wasan kwallon kwandon Amurka Kobe Bryant.

Bryant da ‘yarsa mai shekaru 13 da haifuwa Gianna suna cikin mutane tara da hatsarin jirgi mai saukar ungulu ya rutsa da su jiya Lahadi a wajen birnin Los Angeles.

Rahotannin sun ce suna kan hanyar su ne zuwa kallon wata gasar kwallon Kwando da aka shiryawa matasa.

APTOPIX Clippers Lakers Basketball
APTOPIX Clippers Lakers Basketball

Bryant ya saba amfani da karamin jirgin zuwa filin wasan kwallon kwando daga gidansa a Los Angeles, domin kaucewa mummunan cunkoson motoci a cikin birnin.

Rundunar ‘yan sandan Los Angeles sun ce suna gudanar da bincike a kan musabbabin hatsarin tare da taimakon jami’an tarayya.

A wani takaitaccen sakon Twitter, shugaban Amurka Amurka Donald Trump ya kira wannan batu da mummunar labari, ya yin da uwargidansa Melania Trump ta jajantawa iyalansa.

Shima tsohon shugaban Amurka Barack Obama da aka sani da sha’awar wasan kwallon Kwando ya bayyana alhininsa a wani sakon Twitter.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG