WASHINGTON D.C. —
Rasuwarsa na zuwa ne kwanaki uku bayan rasuwar Stephen Keshi, wanda shima ya horar da ‘yan wasan na Najeriya.
Amodu kasance Darekta ne a hukumar kwallon kafar kasar ta NFF kafin mutuwarsa, mukamin da ya rike tun daga shekarar 2013.
Ya taimakawa Najeriya ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekarun 2002 da 2010, amma an sallame shi kafin fara gasar.