Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yayi Kira Ga Bashar Al-Assad Kan Rikicin Syria


Jakada na musamman Kofi Annan yake ganawa da shugaban Syria Bashar al-Assad a Damascuss.

Ganin ana samun karin mace mace kuma kasashen yammacin duniya suna korar jakadun Syria,Kofi Annan jakadan kasa da kasa ya gayawa shugaba Bashar al-Assad na Syria cewa... ...

Ganin ana samun karin mace mace kuma kasashen yammacin duniya suna korar jakadun Syria,Kofi Annan jakadan kasa da kasa ya gayawa shugaba Bashar al-Assad na Syria cewa shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ba zai sami nasara ba in ba tareda an dauki matakai masu gauni na kawo karshen tarzoma ba.

Kamar yadda kakakin jakadan na musaman ya fada, Mr. Annan ya gayawa Mr. Assad damuwar kasashen duniya kan ci gaba d a zubda jinni da ake yi, ciki har da kisan gillar da aka yi wa maza da mata da yara fiyeda dari a garin Houla makon jiya.

Ofishin hukumar kula da hakkkin Bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva yace masu sa ido sun gano cewa kasa da mutane 20 cikin wan nan adadi ne aka kashe da manyan bindigogi da tankunan yaki. Galibinsu anyi musu kisan gilla ne a gidajensu, wadda aka aza alhakin kan mayakan sakai masu goyon bayan gwamnati.

Sakamakon kisan akalla kasashe tara sun kori jakadun Syria dake kasashen nasu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG