Afirka ta Kudu dai na fama da karuwan matsalar kisar gilla, amma shugabannin al’umma sun ce hukumomi sun yi watsi da Diepsloot, wani gari mai yawan mutane sama da 350,000 a arewacin Johannesburg inda ake samun yawan matsalar kashe-kashe da fyade.
‘Yan sandan sun sheda kaddamar da binciken bayan gano gawarwakin matasa bakwai da aka kona.
A cikin wata sanarwar da kakakin 'yan sandan yankin Laftanar Kanar Mavela Masondo ya aikewa kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP, ya ce an kyankyasa musu labarin gano gawarwaki biyu da aka kona a daren Juma'a.
Ya kara da cewa an agno karin wasu gawarwaki biyar da sanyin safiyar ranar Asabar a wata gunduma dake kusa da garin na Diepsloot.
"Bincike a matakin farko ya nuna cewa wasu gungun jama’a ne suka aikata duk laifukan guda biyu, inda suka yi wa mutanen duka suannan suka kona su," a cewar Masondo.
An gano gawarwakin mutanen biyar, kuma dukkanin su ‘yan kimanin shekaru 20 ne da tarin bulo a kan su a wani fili mai yawan juji.
“Duk an bi su ne, aka kama su, aka daure su kafin a kashe su, haka yake ‘wannan sarkar wuya ce,” in ji wani mazaunin garin, yana nufin yadda aka yi amfani da tayoyi ko igiya da aka daure mutanen kafin aka cinna musu wuta.
Ya kara da cewa “A yau akwai ‘yan sanda da yawa kuma muna fatan za su tsaya saboda muna bukatar su,” in ji mazaunin garin, da ya nemi a sakaya sunansa saboda tashe-tashen hankula a garin. “An yi fashi da yawa kuma mutane sun fusata.
Dandalin Mu Tattauna