Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaman Ousman Ya Gargadi Kasashen Waje Su Daina Taya Bazoum Murnar Cin Zaben Nijar


Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar.
Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar.

Dan takarar jam’iyar adawa ta RDR Canji, Alhaji Mahaman Ousman ya gargadi kasashen waje da kungiyoyin kasa da kasa su daina shishshigi a sha’anin zaben kasar na ranar 21 ga watan Fabrairu don kauce ma zama kanwa uwar gami a wannan lokaci na ja-in-ja a kan sakamakon zabe.

Sakwannin taya murnar lashe zabe da wasu shugabannin kasashen duniya, ciki har da makwabta, suka fara aike wa dan takarar jam’iya mai mulki ne ya sa abokin fafatawarsa, Mahaman Ousman kiran wadanan abokan hulda su mutunta tsarin zaben Nijer a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Dan takarar na kawancen jam’iyyun hamayya ya yi wannan jan hankali ne a ganawarsa da manema labarai a nan birnin yamai.

Karin bayani akan: Bazoum Mohamed, Mahaman Ousman, Kasar Nijar.

Mahaman Ousman ya ce “kamata ya yi a jira a ga hukuncin da kotu zata yanke kafin kasashe da kungiyoyin waje su fara aike wa da sakwanninsu na taya murna, saboda har yanzu ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.”

Mahaman Ousman, wanda a jiya Litinin ya gabatar da takardun korafe korafe a game da yadda yake ganin zaben 21 ga watan Faburairu ya gudana, na fatan kotun ta dubi bukatunsa da idon rahama.

Sakamakon wucin gadin da hukumar zabe ta bayar a ranar 23 ga watan Faburairu ya ayyana Bazoum Mohamed a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 55.75 daga cikin 100 na yawan kuri’u saboda haka kawancen jam’iyun dake goyon bayansa ke cewa suna da kwarin guiwar ba za ta canza zani ba kamar yadda Yahouza Sadissou mai magana da yawun Coalitin Bazoum 2021 ya fada wa Muryar Amurka.

Dokokin Jamhuriyar Nijer sun kayyade wa kotun tsarin mulkin kasa kwanaki 28 don bayyana sakamakon dindindin daga lokacin da hukumar zabe ta fitar da sakamakon wucin gadi.

Ga rahoton wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
XS
SM
MD
LG