Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa: Amurka Za Ta Kai Bukatar Daukan Matakin Soji a Gaban MDD


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley (daga hagu) Mai ba da shawara kan harkar tsaro H.R. McMaster (daga dama)
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley (daga hagu) Mai ba da shawara kan harkar tsaro H.R. McMaster (daga dama)

Wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka biyu, sun ce shugaba Donald Trump, zai mika bukatar a kara tsaurara takunkumin tattalin arziki akan Korea ta Arewa, a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a mako mai zuwa.

Wasu Jami'an gwamnatin Shugaba Donald Trump sun ce shugaban zai gabata da bukata a gaban Majalisar Dinkin Duniya, cewa idan har hanyar diplomasiyya ba ta yi tasiri ba akan Korea ta arewan, to babu makawa, hakan zai kara yiwuwar daukan matakin soji.

A wata ganawa da aka yi a Fadar White House, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley tare da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, H.R. McMaster, sun yi lale marhabin da matakin da aka dauka a wannan watan, na kara kakaba takunkumi akan Korea ta arewa, to amma sun ce duk da haka, har yanzu kasar na ci gaba da nuna halayenta.

McMaster ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai a bi tafarkin diplomasiyya, tare da daukan tsauraran takunkumi, idan har ana so a kaucewa daukan matakin soji.

Tawagar da shugaba Trump zai je da ita babban taron na Majalisar Dinkin Duniya a matsayinsa na shugaban kasa, wani abu ne da ba a saba gani ba, domin ta hada har da Mataimakinsa, Mike Pence da Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson da sauran manyan jami’ai.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG