Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane da yawa a jihar Florida zasu dade ba su da wutar lantarki


Wani mutum yake ratsa ambaliyar ruwa a jihar Florida

Ambaliyar ruwa da datti sun kanainaiye tituna a jihar Florida, haka kuma mahaukaciyar guguwar teku Irma ta katsewa miliyoyin jama'a wutar lantarki.

Mahaukaciyar guguwar teku Irma ta katsewa rabin mutanen jihar Florida wutan lantarki kuma hanyoyi a yankuna da dama na jihar ambaliya da datti sun kanainaiye su.

Gwamnan jihar Florida Rick Scot ya fada a jiya Litinin bayan da yayi shawagi ta kan tsibiran jihar cewa farfadowa daga barnar da Irma tayi zai dauki lokaci mai tsawo.

Ya fadawa yan jarida cewa kimamin ma’aikatan wuta dubu ashirin da uku da karin dubbai da suka je jihar domin taimakawa suna aikin maido da wutar lantarki, to amma yace tilas wasu mutane su yi shirin yin makoni basu da wuta.

An dorawa mahaukaciyar guduwar teku Irma laifin mutuwar mutane biyar a jihar Florida da biyu a jihar Georgia da kuma biyu a jihar South Carlina. Ta kuma kashe akalla mutane talatin da biyar a lokacin data ratsa tsibiran yankin Caribbean a makon jiya.

Ranar Talata shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci tsibiran kasar ta Faransa da mahauciyar guguwar teku Irma ta yiwa barna sosai.

Shugaba Macron ya isa Guadeloupe cikin jirgin da yayi jigilar ruwa da kayayyakin abinci da magunguna da kuma na’urorin aikin gaggawa. Yayi alkawarin cewa za’a yi jigilar karin kayayyakin agaji da tura jami’an tsaro a tsibiran cikin harda tsibiran Saint Martin da Saint Barts idan guguwar ta fi yiwa barna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG