Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Yi Ikrarin Cimma Burinta Na Zama Kasa Mai Makamin Nukiliya


Wani mutum yana kallon akwatin talbijin da ke nuna yadda Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliyanta a ranar 29 ga watan Nuwamba 2017
Wani mutum yana kallon akwatin talbijin da ke nuna yadda Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliyanta a ranar 29 ga watan Nuwamba 2017

Sabon gwajin makamin nukiliya da Korea ta Arewa ta yi, ya nuna cewa ta kara inganta makamin ta yadda zai iya tafiya mai nisan zango, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar.

Gwajin harba makami mai linzami, mai cin dogon zango da Korea ta Arewa ta yi kwanan nan ya kara zafafa zaman dar-dar, yayin da kasar ta sanar cewa yanzu makamanta za su iya kai wa ko ina a Amurka.

Wannan shi ne gwaji na baya-bayan nan cikin watanni biyu da kasar ta yi.

A yau Laraba wani mai sanarwa a talabijin na KRT, mallakar gwamnatin Koriya ta arewa, ya bayyana gwajin makamin.

“An samu nasarar gwajin harba sabon makami mai linzami mai cin dogon zango samfurin Hwasong-15, wanda aka kera bisa shawarar Jam’iyyar Ma’aikata ta Koriya.”

Biyo bayan gwaje-gwajen makaman da Koriya ta arewa ta yi a baya, kasar ta yi ikirarin cewa makaman ta za su iya dira kan kowanne bangaren Amurka.

Amma wannan shi ne karon farko da kasar ta iya cimma haka da sabon makamin da ta kera.

Jami'an Amurka da na Korea ta Arewar sun amince da cewa makamin zai iya yin tashi mai nisan da ya fi wadanda kasar ta gwada harbawa a baya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG