Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Tace Ta Jingine Gwajen-gwajen Nukiliya Da Makamai Masu Linzami.


Shugaba Kim Jon Un.
Shugaba Kim Jon Un.

Wannan sanarwar da hukumomin kaar suka bayar tana zuwa ne kasa da mako daya kamin taron koli tsakanin kasashen koriyoyin biyu.

Koriya Ta Arewa tace ta dakatar gwaje-gwajen makaman Nukiliya, kuma tana shirin rufe sansanin da take yin gwaje-gwajen.

Kamfanin dillancin Labaran hukumomin kasar yace haka nan rundunar mayakan kasar zata tsaida duk gwaj-gwajen makamai masu linzami masu cin dogon zango, kuma dakatarwar ta fara aiki daga Asabar.

Sanarwar tace, gwamnati tana daukar wadannan matakan ne da nufin juwa alkiblar kasar zuwa inganta tattalin arzikinta.

Wannan matakin yana zuwa ne kasa da mako daya gabannin ganawar shugabannin koriyoyin biyu, da zummar kawo kawo karshen rikicin Nukiliyar da suke yi a zirin na Koriya.

Amurka da Koriya Ta Arewa, suna shirin gudanar da tasu taron kolin duk da cewa ba a aje lokaci ba tukuna.

Bayan da Koriya Ta ta bada wannan sanarwar, shugaban Amurka Donald Trump, ya fada a shafinsa na Tweeter cewa "Wannan labari mai yana dakyau ga Koriya Ta Arewa da kuma duniya baki daya," yace yana sa rai kan taron kolin da zai yi da shugaba Kim Jon Un na Koriya Ta Arewa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG