Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tace Dole China Ta Hadu Da Sauran Kasashen Duniya Domin Tsawwala Takunkumi Ga Koriya Ta Arewa


Koriya ta Arewa dai ta batawa sauran kasashen duniya rai, alokacin da ta ce ta gudanar da gwajin bam din hydrogen

Kasar Amurka tace dole ne China ta hadu da sauran kasashen duniya domin tsawwala takunkumi kan kasar Koriya ta Arewa, kan gwajin makaman Nukiliyar ta na baya bayan nan a saboda irin dangantaka ta musamman da take da ita da Koriya ta Arewa.

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, shine yayi wannan kira a yau Laraba, a birnin Seoul lokacin wani taro da ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Koriya ta Arewa dai ta batawa sauran kasashen duniya rai, alokacin da ta ce ta gudanar da gwajin bam na hydrogen na farko da ta taba yi ranar 6 ga watan Janairu, duk da cewa tana cikin wasu takunkumin MDD na aikata ire iren wannan gwaji a baya.

China da Koriya ta Arewa abokaine na kut da kut a fannin harkokin difilomasiya da kasuwanci, amma wannan dangantaka tasu ta yi tsami alokacin da Koriya ta Arewa ta kasa yin watsi da burin ta na mallakar makaman Nukiliya.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG