Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Zata Gasar 'Olympic' A Koriya Ta Kudu


Shugaban tawagar Koriya ta Arewa Ri Son Gwon (Hagu) da takwaransa na Koriya ta Kudu Cho Myoung-gyon (Dama)
Shugaban tawagar Koriya ta Arewa Ri Son Gwon (Hagu) da takwaransa na Koriya ta Kudu Cho Myoung-gyon (Dama)

Bayan kai komo tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu, yanzu Koriya ta Arewan ta amince ta aika 'yan wasanta zuwa wasan Olympic da zai wakana a makwafciyarta da a da can suka kwashe shekaru da dama suna yakar juna.

Koriya ta Arewa ta yarda cewa za ta aika tawagar ta zuwa gasar Olympic wata mai zuwa a Pyeongchang da ke Koriya ta Kudu. An yi wannan tayin ne yau Talata yayin wata ganawa da aka yi ta kiki da kika tsakanin Koriya ta Arewa mai tsarin mulkin Kwaminisanci da Koriya ta Kudu mai tsarin mulkin diflomasiya.

Sun yi zaman ne a Panmunjom, wani kauyen da aka radawa suna kauyen zaman lafiya da ke kan iyakar kasashen biyu, inda suka rattaba hannu akan takadar kare yakin shekarar 1953 da suka gwabza da juna.

Chun yace Koriya ta Kudu ta bada shawarar hada dangin wadanda suka rabu tun shekarar 1950 zuwa 1953 lokacin yakin da yayi sanadiyar rabuwa tsarin mulkin mallaka da na Arewa da mulkin diflomasiyya na Kudu da za ayi a sabuwar shekarar Luna.

Bangaren na Arewa ya kuma bada shawarar ganawar soji domin hana duk wani hatsarin da zai janyo tashin hakali akan iyakar. Bangarorin biyu sun yarda cewa za’a dawo da layin waya na soja da Koriya ta Arewa ta yanke kusan shekara daya kenan, bayan Koriya ta Kudu ta rufe ayyukan da take yi a wani kamfani dake tsallake Kaesong akan iyakar kasashen biyu.

Koriya ta Arewa ta bude layin wayar bayan ‘yan sa’o’i kadan da ganawarsu, kuma zata fara aiki gadan gadan ranar Laraba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG