Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Sake Wani Gwajin Makami Mai Muhimmaci


Kim Jong Un
Kim Jong Un

Koriya ta Arewa ta ce ta gudanar da wani gwaji mai muhimmanci a wata tashar harba tauraron dan Adam domin ‘kara karfin makamin Nukiliyarta.

Gwajin makamain da Koriyar ta yi na zuwa ne gabannin cikar wa’adin zuwa karshen shekarar nan da kasar ta sakawa kanta, kan cewa Amurka ta sassauta matsayarta kan tattaunawar Nukiliya, a tsakiyar barazanar da take yi na dawo da gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango ko gwajin Nukiliyar ta.

Kamfanin dillancin labaran Koriya bai fadi irin makamin da aka gwada ba na yau Asabar, haka kuma bai fitar da hotuna ba.

Koriya ta Arewa ta yi gwajjin makamai masu linzami masu cin gajeran zango har 13 tun watan Yuni. Masu nazari dai sun yi hasashen cewa nan bada dadewa ba Koriyar za ta yi amfnai da tashar Sohae wajen harba tauraron dan Adam sararin samaniya ta hanyar amfani da fasahar harba makamai masu cin dogon zango.

Karkashin dokokin Majalisar Dinkin Duniya an haramtawa Koriya ta Arewa duk wasu ayyukan makamai samfurin ballistic, amma a baya tana yin amfani da su ta hanyar fakewa da abin da ta kira ayyukan tauraron dan Adam wajen yin amfani da fasahar makamai masu cin dogon zango.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG