Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Saki Amurkawa Uku Da Ke Hannunta


Amurkawan da aka sake

Wani babban jami’in gwamnatin Amurka da ke wurin da aka saki fursunoni a Birnin Pyongyang ya gaya ma manema labaran da ke cikin tawagar Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo cewa wani jami’in Koriya Ta Arewa ya gaya ma mike Sakataren Harkokin Wajen na Amurka cewa Shugaba Kim ya yi ahuwa ma Amurkawan nan uku da ke hannun Koriya Ta Arewa.

An kai mutanen da aka sake din jirgin saman da Sakataren Harkokin Wajen Amurka ke amfani da shi, kuma “sun taka ne da kafarsu zuwa wurin jirgin ba tare da an rike su ba,” a cewar wata takardar bayani ta Fadar White House.

Wadanda aka daure da din na kan hanyarsu ta zuwa Amurka bayan sun yada zango a karamin filin jirgin saman Yokota na Japan. Su na tafiya ne cikin wani jirgi dabam da na Pompeo.

Da Tony Kim da Kim Hak Song na koyarwa ne a jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Pyongyang lokacin da aka kama su a lokuta daban-dabam a 2017, bayan an zarge su da take-taken zagon kasa ga kasar da kuma kokarin fifar da gwamnati.

Da ukun mai suna Kim Dong Chul, an kama shi ne a Rason da ke kuryar arewa maso gabashin Koriya Ta Arewa a 2015 aka kuma zartas masa da daurin shekaru 10 tare kuma da horo mai tsanani shekara guda bayan an same shi da laifin yin leken asiri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG