Koriya Ta Arewa ta soke muhimmiyar tattaunawar da aka shirya cewa za ta yi jiya Laraba da Koriya Ta Kudu, sannan ta ce ya rage ga Amurka ta kula da makomar ganawar da za a yi tsakanin Shugaba Kim Jong Un da kuma Shugaba Donald Trump saboda atisayen hadin gwiwa tsakanin Koriya Ta Kudu da Amurkar.
Kamfanin Dillancin Labaran Koriya Ta Arewa ya ce atisayen, mai lakabin “Max Thunder” ba wani abu ba ne illa koyon dabarun mamaye Koriya Ta Arewa da kuma takala duk kuwa da irin cigaban da aka samu a dangantakar Koriya Ta Arewa da Koriya Ta Kudu.
Fadar Shugaban Amurka ta White House dai ba ta yi magana sosai ba illa kawai cewa da ta yi za ta cigaba da tattaunawa da kawayenta.
Facebook Forum