Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Tace Ba Zata Yi Amfani Da Nukiliya, Amma.....


A tsakiya shugaban koriya ta kudu Kim Jong Un ne ake yiwa tafi a babban taron jam'iyyar ma'aikata mai mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya Ta Arewa yace shugaban kasar, Kim Jong Un, ya gayawa taron koli na jam'iyyar ma'aikata mai mulkin kasar cewa, kasarsa ba zata taba amfani da makaman Nukiliya ba, sai idan wata kasa mai nukiliya ta yiwa diyaucinta barazana.

Haka nan kamfanin dillancin labaran da ake kira KCNA a takaice, yace Kim yace a shirye kasar take ta kyautata dangantaka da kasashen da basa shiri da hukumominta dake Pyongyang, ya kara da cewa shugaba Kim, yayi kira da a gudanar da shawarwari da makwabciyarta Koriya Ta Kudu, domin sassauta rashin yarda, da assasawar hakan.

Babu tabbas ko wannan alkawari da shugaba Kim Jong Un yayi, alamace ta canji daga halayenta na bijirci ga makwabtanta da kuma Amurka. A cikin watan Maris, Koriya Ta Arewa tayi barazanar "ba tareda wani gargadi ko jan kunne ba" zata farwa Amurka da Koriya Ta Kudu da makaman Nukiliya, farmakin "kan mai uwa da wabi," a zaman martani kan atisayin soja na hadin guiwa da kasashen biyu suke yi.

A Koriya ta Kudu masu sa ido suna cikin shirin ko ta kwana, kan rahotannin da suke nunin cewa, Koriya ta Arewa tana shirin gudanar da gwajin makamin Nukiliya karo na biyar.

A watan Maris. MDD ta kara tsaurara takunkuman karya tattalin arziki data azawa Korita ta Arewa, bayan da kasar ta gudanar da gwajin Nukiliya karo na hudu.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG