Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Za Ta So Ganawa Da Amurka - inji Koriya Ta Kudu


Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jung Un
Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jung Un

Rigimar yankin ruwan Koriya ta dau wani sabon salo da ka iya sa kura ta lafa, bayan da Koriya Ta Kudu Ta ce Koriya Ta Arewa za ta so ganawa da Amurka.

Jami’an kasar Koriya Ta Kudu sun ce Koriya Ta Arewa za ta so tattaunawa da Amurka, duk kuwa da kalaman caccaka na baya-bayan nan daga Koriya Ta Arewar.

Ofishin Shugaban kasar Koriya Ta Kudu ya ce an yi wannan bayanin ne lokacin da Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in ya gana da tawagar Koriya Ta Arewa ta wasan Olympics, inda dukkannin bangarorin su ka amince cewa ya kamata a samu hulda tsakanin Koriyawan, da kuma tsakanin Amurka da Koriya Ta Arewa a lokaci guda.

Tun da farko wani martani daga kafar labaran gwamnatin Koriya Ta Arewa ta KCNA ya ce takunkumin da Amurka ta kakaba ma Koriya Ta Arewa na baya-bayan nan, tamkar kaddamar da yaki ne.

Martanin ya zargi Amurka ta tayar da fitina a yankin ruwan Koriya, sannan ya yi nuni da cewa Koriya Ta Arewa fa na da makaman nukiliya da ka iya tinkarar duk wata barazana daga Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG