Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Kudu ta Kira Taron Gaggawa Akan Makwabciyarta Ta Arewa


Koriya ta Kudu ta kira wani taron gaggawa tare da neman makwabciyarta ta arewa da ta mutunta wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla.

Hakan na faruwa ne sa’o’i bayan da Koriya ta Arewa ta yi barazanar ruguza wani ofishin da aka kafa domin tuntubar juna a tsakanin kasashen biyu, da kuma barazanar daukan matakin soji akan Koriya ta Kudu.

Akwai rahatonni da ke nuna damuwar cewa akwai yiwuwar Koriya ta arewa ta koma takalar fada ne domin jaddada hadin kan kasar, yayin da tattaunawar da suke yi da Amurka kan makamin nukiliyanta ya cije a wani mataki.

Masu lura da al’amura sun ce Koriya ta Arewa na matukar bukatar a sassauta mata takunkumin da aka kakaba mata wanda Amurka ke jagoranta, yayin kuma da ake fuskantar matsalar annobar coronavirus.

Ita dai Koriya ta Arewa na zargin makwabciyarta ta Kudu da gazawa wajen hana masu fafutuka da ke farfagandar cusa kiyayyar gwamnati a zukatan ‘yan koriya ta arewa, wadanda ke tsallakawa zuwa cikin yankinta domin raba takardu na farfaganda.

Amma kwararru sun ce, Koriya ta Arewa ta damu matuka ne saboda Koriya ta Kudu ba ta tabuka komai bwajen ganin an farfado da ayyukan bunkasa tattalin arziki da kasashen biyu ke hada kai su yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG