Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Daliban Najeriya Ba Su Gaggawar Gudu Daga China


 Wani asibitin kula da murar 'koronabairus' a China
Wani asibitin kula da murar 'koronabairus' a China

Duk kuwa da gaggawar yaduwar da mugunyar cutar nan mai saurin kisa ta "koronabairus" a kasar China, daliban Najeriya ba su gaggawar dawowa gida Najeriya.

A hirar da aka yi da wani shugaban kungiyar daliban Najeriya a kasar China mai suna Ibrahim Lawandi Datti game da cutar mura ta Coronavirus ya ce zuwa safiyar jiya Laraba, alkaluma sun nuna cewa mutane wajen 44,666 sun kamu da wannan cuta ta coronavirus. Sannan ana kyautata zaton an killace wasu mutanen kuma wajen 21,675 da ake ganin mai yiwuwa ne sun kamu da cutar, ana nan ana sa ido kansu don tabbatar da halin da su ke ciki. Sannan zuwa yanzu mutane wajen 1,114 sun mutu zuwa safiyar jiya Laraba; sai dai akwai mutane wajen 4,703 wadanda su ka warke zuwa jiya Labarar kuma har an sallame su daga asibiti.

Da Mahmud Lalo ya tambaye shi ko shin gaskiye ne cewa dalibai na kira ga gwamnatocin kasashensu da su je su kwashe su, sai ya ce akasari ‘yan kasuwa ne ke irin wannan kiran, kuma bincike ya nuna yawancin dalibai kan ce zamansu a China ya fi masu rufin asiri. Ya ce kasar China, a misali, ta fi Najeriya karfin tattalin arziki da kuma kwararrun da ka iya jinyar cutar. Don haka dalibi dan Najeriya ba zai so a mayar da shi Najeriya a killace shi na tsawon lokaci babu kulawar kirki ba.

Ya ce idan an kai dalibi gida Najeriya kuma cutar ta coronavirus ta kare wa zai dawo da dalibin China? Ya ce hasali ma, zuwa yanzu a duk fadin kasar babu inda aka tabbatar cutar ta shiga wata makaranta.

To saidai shugaban daliban ya nuna alamar takaita zirga-zirgar da aka yi na takura daliban. Ya ce wannan ya sa kudin da daliban ke bukata don zaman gari ya ninku. Ya ce Ofishin Jakadancin Najeriya ya yi kokari sosai saboda tun aukuwar annobar Ofishin Jakadancin Najeriya da shugabannin dalibai Najeriya ke ta tuntubar juna. Ya ce tuni ma jakadan Najeriya a China, Baba Ahmad Jidda ya cire kudi Naira miliyan guda daga aljihunsa ya ba daliban Najeriya a matsayin gudunmowa kafin gwamnatin Najeriya ta kawo dauki.

Ga cikakkiyar hira da Shugaban daliban, wanda aka fara da tambayarsa halin da ake ciki a China, sai ya yi bayani kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:47 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG