Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Chana Ta Samu Attajiri da Laifin Kisa


​Wata kotu kasar China ta samu wani rikakken attajirin kasar China da laifin yi kisa a saboda haka ta yanke masa hukuncin kisa.

Yau juma'a wannan kotu dake tsakiyar lardin Hube ta bada sanarwar cewa an samu Liu Han da kaninsa Liu Wei da laifin shiryawa da jagorancin wata kungiyar makisa irin ta mafia mai wakilai talatin da shidda, dake da alhakin kashe akalla mutane takwas.

An zargi wa da kani da kuma wasu mutum talatin da hudu da laifin aikata laifuffuka, ciki harda taka rawa a aikata laifuffuka da kuma yin kisa da niya.

Haka kuma ana zaton cewa ita wannan kungiya ta makisa tana da alaka da manyan yan kasuwa da yan siyasa a Sichuan.
XS
SM
MD
LG