Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Amince Abduljabbar Ya Nemi Sabbin Lauyoyi Bayan Da Masu Kare Shi Suka Janye


Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

A kwanakin baya kotu ta ba da umarnin a gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwar Sheikh Abduljabbar, wanda sakamakon bincike ya nuna cewa lafiyarsa kalau kamar yadda rahotanni suka nuna.

Tawagar lauyoyin da ke kare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a karar da aka shigar da shi kan zargin yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W a Kanon Najeriya, ta ce ta janye daga aikin kare malamin da take yi a kotu.

Cikin wata wasika da suka gabatarwa kotun, Saleh M. Bagoro, H.G Magashi, Bashir Sabiu, R.S Abdullahi da Y.A Umar, sun ce sun yanke shawarar janyewa daga aikin kare shi ne bayan da suka tattauna da Abduljabbar a cewar jaridar Daily Nigeria.

Rahotanni sun ce tuni Alkali Ibrahim Sarki Yola da ke sauraren karar ya amince da janyewar lauyoyin.

Bayanai sun yi nuni da cewa, kotun ta ba malamin damar ya nemi wasu lauyoyi bayan da ya bukaci hakan.

A ranar Alhamis tawagar lauyoyin ta mika wannan bukata amma ba ta fadi dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki ba.

Janyewar lauyoyin na zuwa ne, yayin da aka gabatar da rahoton binciken lafiyar kwakwalwar Abduljabbar wanda ya nuna cewa lafiyarsa lau.

A kwanakin baya kotun ta ba da umarnin a gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwar malamin.

Alkalin kotun ya dage sauraren karar zuwa 30 ga watan Satumba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG