Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukabalar Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano


Wasu daga cikin malaman da suka halarci wajen taron mukabalar da aka yi

Ana gudanar da mukabala tsakanin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara da sauran malaman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Zaman mukabalar na wakana ne a ma’aikatar shari’ar jihar ta Kano wacce aka fara tun da safiyar ranar Asabar.

Kamar yadda rahotanni ke nunawa, ba a nuna wannan mukabala kai-tsaye ta kafafen yada labarai, sabanin yadda aka tsara za a yi a baya.

Sannan binciken da Muryar Amurka ta yi, ya gano cewa wadanda aka aikawa da takardar gayyata ne kadai aka bari suka shiga wajen taron.

A baya gwamnatin jihar Kano ta saka ranar 7 ga watan Maris na wannan shekara, a matsayin ranar da za a gudanar da mukabalar a fadar Sarkin Kano, amma daga baya a dage zaman bayan wani umarnin kotu.

Idan za a iya tunawa a watan Fabrairun wannan shekara ne gwamantin Kano, ta dakatar da malamin daga gudanar da karatu a makarantarsa saboda da zarginsa da yin batanci ga Annabi (S.A.W.,) zargin da Shekih Kabara ya musanta.

Dalilan da suka sa gwamnatin jihar Kano daukar matakin rufe masallacin da su ne, "kalamansa na nuna kaskanci ga Annabin Rahma, Annabi Muhammdu {SA}" a cewar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje cikin wata tattaunawa ta mussamman da Muryar Amurka.

Matakin ya biyo ne bayan da wasu malamai na jihar ta Kano, da suka ja hankali akan cewar, hakan na iya haifar da hatsaniya, don haka gwamnati ta ga cewar akwai bukatar daukar matakin.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG