Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ba Da Belin Ali Ndume


Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar dattijan Najeriya
Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar dattijan Najeriya

Babban kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin Sanata Ali Ndume, amma bisa wasu sharudda da ta gindaya.

Mai shari’a Okon Abang ya amince da bukatar neman belin Ndume bayan bayani mai tsawo da ya yi nazari a kan hujojjin da lauyoyin bangaren hukumar EFCC da na wanda a ke kara (Ndume) bisa sharudda suka gabatar na kare shari’arsu.

A cikin sharuddan da mai shari’a Abang ya gindaya da suka hada da mika fasfon fita kasashen waje na Ndume ga magatakardar kotu.

Snnan an bukaci ya kawo wanda zai tsaya ma sa da ke da kaddara a birnin tarayya Abuja da takardun kaddarar, sannan rubuta wasika ga kotu da takardun zama da aka yi daga watan Oktoba zuwa Nuwamba da mu ke ciki, da sauran takardun da kotu ke bukata daga shi wanda aka ba da belin nasa cikin kwanaki 10.

Lauya da ke kare Ndume, Marcel Oru, ya ce za su bi kadin shari’ar bisa matakan da kotu ta tsara tare da mika godiya ga mai shari’a Abang da daukar matakin ba da belin wanda ya ke kare wa.

Mallam Muhammad Askirama, dan mazabar da Sanata Ndume ke wakilta da ke zama daya daga cikin wadanda suka halarci zaman kotu ya yi murna kan samun belin Sanata Ndume.

A yayin da wasu mutane ke murna a kan samun belin, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Abubakar Muhammad Saraki, ya ce akwai lauje cikin nadi kan belin.

Kotun da mai shari’a Okon Abang ke jagoranta ta yi watsi da hujjojin da lauyoyin bangaren EFCC suka gabatar na kotu ta ki amincewa da bukatar neman belin Ndume, kuma ta ce ta ba wa sanata Ali Ndume dama daban-daban na kawo Abdulrasheed Maina, gaban kotu tun daga ranar 2 zuwa 19 ga watan Oktoba da 18 ga watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki, don ci gaba da sauraron karar zargin da ake masa kafin nan ta ba da umarnin a tsare shi a gidan kaso da ke yankin Kuje a birnin taraya Abuja.

Abin jira a gani shi ne yadda lauyoyi da mukarraban sanata Ndume za su bi kadin matakin kotu tare da cika sharuddan da ta bayar domin sakin wanda ake kara.

XS
SM
MD
LG