Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ce Hukunci Da Fara Ministan Birtaniya Ya Dauka Ya Sabawa Doka


A yau Laraba wata kotu a kasar Scotland ta yanke hukunci cewa matakin da Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ya dauka na dakatar da majalisar dokokin kasar ya sabawa doka.

Alkalan ba su ba da umarnin dakatarwar ba, amma a maimakon haka sun ce akwai bukatar Kotun koli ta Biritaniya ta yanke wannan hukunci.

Gwamnati ta nuna adawa da wannan hukuncin na kotun, sannan ta ce za ta daukaka kara.

An dakatar da zaman majalisar na tsawon makonni biyar ya fara aiki daga jiya Talata.

'Yan adawa sun nuna adawa ga abin da suka kira "juyin mulki" daga Johnson, yayin da Birtaniyya ke fuskantar wa'adin ficewa daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga Oktoba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG