Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dakatar Da Bukatar Soke Zargin Aikata Manyan Laifuka Akan Micheal Flynn


Wani alkali a Amurka ya dakatar da wata bukatar ma’aikatar shari’ar kasar na soke zargin aikata manyan laifuka da ake yi wa tsohon mashawarcin tsaron gwamnatin Trump Micheal Flynn, domin baiwa kwararru masu zaman kansu a fannin shari’a damar nazari akan matakin ma’aikatar.

Alkali Emmet Sullivan a yammacin jiya Talata ya ce, za a baiwa abokan aikin kotun damar gabatar da bayanansu, haka kuma za’a shata wani lokacin da ya dace na sauraren bayannan su.

Sullivan na iya kiran shaidu su bada bahasi tare da amsa tambayoyi game matakin da ma’aikatar shari’ar ta dauka a makon da ya gabata na janye tuhumar aikata manyan laifuka da ake yi wa Flynn, da abin da ka iya mai da shari’ar sabuwa ‘yan watanni gabanin zaben shugaban kasa.

Lauyoyin Flynn sun ki amincewa da yunkurin na Sullivan, inda suka ce bai kamata wani ya tsoma bakinsa a cikin wannan shari’a ba.

“Shari’ar manyan laifuka na gudana tsakanin Amurka da wanda ake zargi ne kawai. Babu inda aka baiwa wani damar tsoma baki cikin shari’ar, kuma baza ayiwa dokar kasa karan tsaye ba”, a cewar masu kare Flynn.

Zarge-zargen da ake wa Flynn, na daga cikin binciken da Robert Mueller ya gudanar kan sa hannun Rasha a zaben shugaban kasa na shekarar 2016.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG