Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Hana Belin Nnamdi Kanu, Ta Bada Umarnin Hanzarta Sauraran Shari'arsa


Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu
Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu

Mai Shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Abuja, ta hana bada belin jagoran haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

WASHINGTON DC - Saidai, kotun ta bada umarnin hanzarta sauraran shari'arsa, inda yake fuskantar tuhume-tuhumen dake da nasaba da cin amanar kasa.

Kanu, wanda ya gurfana a gaban kotun a yau Talata, ya kasance a hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS tun sa'ilin da aka kama shi a watan Yunin shekarar 2021.

Da take zartar da hukuncin, Mai Shari'a Binta Nyako ta bayyana cewar kotu za ta hanzarta sauraran karar ne kawai, sa'annan ta bukaci bangaren masu shigar da kara su gabatar da shaidansu na farko.

Lauyan Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor ya bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin. Inda ya ce lauyoyin jagoran kungiyar ta IPOB ba za su ci gaba da shari'ar ba matukar ba'a basu damar tattaunawa da mutumin da suke karewa ba.

Ejimakor ya kara da cewar, tattaunawarsu da Kanu abune mai wahalar gaske a yayin da yake tsare a hannun Hukumar DSS saboda ana sauraran dukkanin hirarsu kuma har yanzu Kanu na sanye ne da tufafin da aka kama shi dasu, duk kuwa da cewar ta bada umarnin ya sauya su.

Ya kuma yi zargin cewar ana tauyewa wanda yake karewa hakkokinsa abinda yace ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya kuma bayyana rashin gamsuwar lauyoyin Nnamdi Kanu tare da bukatar a dakatar da sauraran shari'ar har sai sun gana da wanda suke karewa, bukatar da kotun ta amince da ita.

Kanu ya bukaci a bashi damar gabatar da jawabi ga kotun kuma aka amince da inda ya shaidawa kotun cewar ya kamu da ciwon zuciya kuma baya samun kulawar data dace karkashin Hukumar DSS.

Don haka ya bukaci a maida shi gidan gyaran hali na Kuje ko kuma ayi masa daurin talala a gidansa, bukatun da mai shari'a Binta Nyako tayi fatali dasu tare da dage sauraran shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Afrilu mai kamawa domin fara sauraran karar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG