Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Hana INEC Kammala Tattara Sakamakon Zaben Jihar Bauchi


Mata Da Nakasassu Suna Cikin Wadanda Suka Fito Zabe
Mata Da Nakasassu Suna Cikin Wadanda Suka Fito Zabe

Babbar kotun tarayya dake Abuja karkashin mai shara’a Ekwo Ejembi ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dakatar da shirin tattara bayananai da kuma kidayar kuri’un data shirya gudanarwa a yau na zaben gwamna a zaben da aka gudanar a karamar hukumar Tafawa Balewa a ranar 9 ga wannan watan.

Kotun ta tsayar da gobe laraba 20 ga wannan watan domin fara sauraron karar da gwamnan jihar Bauchin, Muhammed Abdullahi Abubakar da kuma jam’iyarsa ta APC suka shigar a babban kotun dake Abuja suna kalubalantar.

Dama hukumar zaben ta shirya fara tara sakamakon zaben da aka gudanar a karamar hukumar ne yau Talata, bayan sanar da cewa bata kammala zabe a jihar ba kamar yadda ta sanar a wadansu jihohi shida na Najeria da suka hada da Bauchi, Benuwe, Adamawa, Plateau, Kano, da kuma Sokoto.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG