Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Hana INEC Sa Ido A Zaben PDP


Rundunar ‘yan Sanda ta shirya tsaf, suke domin ganin taron ya gudana lafiya.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a Najeriya, tace zata gudanar da babban taron ta na kasa domin zaben shuwagabani, a birnin Fatakol dake jihar Rivers.

Sai dai kuma wannan taron yazo da sarkakiyar shara’a tada haramta a gudanar da taron, zuwa yanzu dai shuwagabanin jam’iyyar PDP, sun ce basu samu wani umarni ba daga kotu na haramta taron.

Tsohon gwamnan jihar Neja Dr. Mu’azu Babangida Aliyu, wanda ke cikin kwamitin taron yace idan kotu ta dakatar da irin wannan abubuwa akan bada takarda daga shuwagabanin jam’iyyar na yanzu babu wanda yace ya karbi wani takarda daga kotu na dakatar da wanna taro, amma idan kotu ta bada umarni tilas ne abi kotu.

Babban taron jam’iyyar PDP, da zai gudana ranar Asabar mai zuwa na fuskantar kalubale na rashin shighar hukumar zaben Najeriya, INEC.

Kakakin hukumar INEC, Mr. Nick Dazan, yace jam’iyyar PDP, bukaci INEC, ta halarci wanna taro amma kuma tuni INEC, ta zabe jami’an da zasu wakilceta amma sai kotu ta bada umarnin dakatar da zabe da za’a yi, na matsayin Shugaba da sakatare da kuma na mai binciken yadda ake kashe kudade, kuma kotun tace kada INEC, ta ido akan wadanna zabubbuka guda uku, kuma kada INEC, ta amimce da sakamakon akan wadannan zabubbuka uku.

Zuwa yanzu dai birnin Fatakol, yadauki harami inda kawo yanzu ‘yan jam’iyyar ta PDP, daga sassa daban daban na Najeriya, suka ci gaba da kwararowa birnin domin halartar taron.

Rundunar ‘yan Sandan jihar Rivers, ta bakin kakakinta DSP, Ahmed Kidaya Muhammad, ya tace a shirya tsaf, suke domin ganin cewa taron ya gudana lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
XS
SM
MD
LG