Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Hukunta Tsohon Shugaban Kasar Tunisia


Tsohon shugaban kasar Tunisia Zine al-Abidine Ben Ali lokacin da ya ziyarci Mohammed Bouazizi matashin da ya kona kan shi don kuncin rayuwa, wanda kuma shi ne mafarin boren juyin juya hali a kasashen Larabawa

Wata kotu ta yankewa Zine al-Abidine Ben Ali daurin rai da rai

Wata kotun kasar Tunisia ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga shugaban kasar da aka kora daga mulki Zine al-Abidine Ben Ali saboda rawar da ya taka cikin kisan masu zanga-zanga a bara lokacin da aka yi boren da ya haifar da zanga-zangar juyin juya hali a duk fadin yankin Gabas ta Tsakiya.

Ranar Laraba, kotun wadda ke garin Kef ta hukunta tsohon shugaban kasar a bayan idon shi saboda ya na zaman gudun hijira a kasar Saudiyya. Har yanzu dai gwamnatin kasar Saudiyya ta ki mika Ben Ali da uwargidan shi ga hukumomin kasar Tunisia.

Juyin juya halin kasar Tunisia da ya barke a watan Disemban shekarar dubu biyu da goma ya tursasawa shugaban kasar mai kama karya rantar ta kolo ya arce daga kasar wata daya daga bisani. Abun da ya faru a kasar Tunisia ya haifar da juyin juya hali a kasashen Larabawan kusan duk yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka.

XS
SM
MD
LG