Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Jaddada Nasarar Adeleke A Zaben Gwamnan Osun


Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke

A ranar 16 ga watan Yulin 2022 aka gudanar da zaben na Osun, inda   Adeleke ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30 da ke jihar, nasarar da Oyetola ya kalubalanta.

Kotun daukaka kara da ke Abuja a Najeriya, ta jaddada nasarar da gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya samu a zaben gwamnan da aka yi a bara.

A watan Janairu, kotun da ke sauraren kararrakin zabe a jihar ta Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce tsohon gwamna Gboyega Oyetola ne ya lashe zaben.

Hakan ya sa Adeleke ya garzaya kotun daukaka kara da ke Abuja.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Shu’aibu, ta ce dan takarar jam’iyyar APC tsohon Gwamna Oyetola, ya gaza gabatar da hujjojin da za su nuna shi ya lashe zaben, saboda haka, Adeleke na PDP ne ya yi nasara.

A ranar 16 ga watan Yulin 2022 aka gudanar da zaben na Osun, inda Adeleke ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30 da ke jihar.

Hukumar zabe ta INEC ta ce, Adeleke ya samu kuri’a 403,371, yayin da Oyetola ya samu 375,027.

Hakan ya sa Oyetola ya kalubalanci sakamakon zaben a kotun da ke sauraren kararrakin zabe a jihar, wacce a karshe ta ce shi ya ci zaben.

XS
SM
MD
LG