Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sake Dage Zaman Sauraron Shari’ar Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu Da daya daga cikin lauyoyinsa, Ejimako a cikin kotu.
Nnamdi Kanu Da daya daga cikin lauyoyinsa, Ejimako a cikin kotu.

Dage sauraron shari’ar Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan tawagar lauyoyinsa sun gudanar da wani tattaki kan matakin da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka dauka na hana wasu daga cikin lauyoyinsa damar shiga cikin kotun.

Babbar kotun tarayya dake da zama a birnin Abuja ta sake dage sauraron shari’ar shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu, zuwa ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2022.

Dage sauraron shari’ar Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan da tawagar lauyoyinsa suka gudanar da wani tattaki kan kin amincewar da jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS suka yi na baiwa wasu daga cikin lauyoyinsa damar shiga cikin kotun.

Kanu, wanda aka shigar da shi cikin kotun da misalin karfe 9 da mintuna 52 na safiyar Laraba, ya yi Allah wadai da rashin barin wasu lauyoyinsa shiga domin sauraren zaman kotun da jami’an tsaro suka yi, musamman lauyan da ya taso tun daga kasar Amurka, Bruce Fein.

Shugaban na IPOB ya shaida wa kotun cewa Mista Fein, wanda shi ne lauyan da ke kare shi a wata shari’ar sa a Amurka, ya zo don ya shaidi zaman shari’ar da ake yi masa a Najeriya.

Daga bisani kotun taraya karkashin mai shari’a Binta Nyako ta yi masa tambaya don tabbatar ko da yana shirye a fara sauraron shari’arsa ba tare da lauyoyinsa a cikin kotu ba, to amma Kanu ya mayar da martanin kin amincewa da ci gaba da shari’ar.

To sai dai lauyan gwamnatin tarayya, Mohamed Abubakar, wanda shine daraktan shigar da kararraki na gwamnatin kasar, ya bukaci kotun da ta ci gaba da shari’ar ba tare da dukkanin lauyoyin Kanu ba.

Abubakar ya shaida wa kotun cewa a bisa ka’ida, an tsayar da batun ne domin sauraron bukatar da wanda ake tuhuma ya shigar kan ci gaba da tsare shi.

Abubakar ya kara da cewa tun da babban lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor, wanda tun farko yana cikin kotun, ya fita da tawagarsa da zimmar nuna bacin ransu a game da kin barin lauyoyin da yawa su shigo kotu jim kadan kafin isowar alkali, sai a yi watsi da bukatar da ya ke nema.

A hukuncin da ta yanke duk da cewa mai shari’a Nyako ta nuna rashin jin dadinta kan yadda lauyoyin Kanu suka fita daga cikin kotun, amma ta ki karba bukatar da lauyan gwamnati ya ce a yi watsi da ita, sai dai ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2022 domin ci gaba da zaman shari’ar.

XS
SM
MD
LG