Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Soke Nasarar Abba Kabir Yusuf Na NNPP A Zaben Gwamnan Jihar Kano


Engr. Abba Kabir Yusuf
Engr. Abba Kabir Yusuf

Cikin tsauraran matakan tsaro irin na ba sabun ba, a yau Laraba kotun sauraran kararrakin zabe ta yanke hukunci kan korafin sakamakon zaben gwamnan Kano.

Kotun sauraron karar zabe a jihar Kano ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano na watan Maris din 2023, inda ta soke nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu.

Kotun ta kuma bayar da umarnin a janye takardar shaidar cin zabe da INEC ta mika wa Abba Kabir Yusuf tare da bayar da takardar shaidar cin zabe ga Gawuna.

Nasiru Gawuna
Nasiru Gawuna

Jam’iyyar APC ce ta shigar da kara gaban kotun tana kalubalantar nasarar da Jam’iyyar NNPP tayi a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris na bana.

Tun a jiya Talata ne aka jibge dinbin Jami’an tsaro a muhimman wurare na sassan birnin Kano. Jami’an sun hada da sojoji da ‘yan sanda, da dakarun tsaro na Civil Defense, da kuma Jami’an farin kaya na hukumar DSS.

Jami’an tsaron suna sunturi a birnin Kano
Jami’an tsaron suna sunturi a birnin Kano

Tun da almurun jiya ne jami’an suka rinka sintiri a bangarorin birnin na Kano, al’amarin da wasu ke gani wani mataki ne na tabbatar da doka da oda, a gabani da kuma bayan sanar da hukuncin kotun.

A hannu guda kuma, magoya bayan Jami’yyun da ke fafatawa a kotun ne suka yi dafifi a wasu kofofin shiga birnin Kano da kuma wasu muhimman wurare suna dakon yadda zata kasance.

Shaguna da kantuna duk sukan rufe a birnin Kano
Shaguna da kantuna duk sukan rufe a birnin Kano

Baya ga haka, galibin makarantun Kano, musamman na sakandare da Firamare sun kasance a kulle, yayin da kalilan din da suka bude domin daukar darasi suka umarci dalibai da su koma gida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, ba’a bude cibiyoyin hada-hadar kasuwanci, shaguna da kantuna ba a wasu bangarori na Kano, yayin da a gefe guda kuma, babu ababen hawa sosai akan manyan titinan birnin, duka a kokarin kaucewa abin da ka iya faruwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG