Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Tsige Shugabar Korea ta Kudu


Shugabar Korea ta Kudu, Park Geun-hye
Shugabar Korea ta Kudu, Park Geun-hye

Kotun kundin tsarin mulki ta Koriya ta Kudu ta kad'a kuri'ar da aka sami gagarumin goyan bayan tabbatar da tsige Shugabar kasa Park Geun-hye.

Mai rikon mukamin Babban Alkali Lee Jung-mi ya karanta hukuncin da aka yanke daga kotun kundin tsarin mulkin kasa dake Seoul a yau Juma’a wanda aka yada shi kai tsaye a kafafen yada labarai na kasar.

Lee Jung-mi ya ce “Mun hakikance cewa, akwai riba mai yawa wajen sauke wadda ake tuhuma daga ofishi. Saboda haka, da murya daya ta alkalancinmu mun goyi bayan tsigewar. An kori Shugabar kasa Guen -hye."

Duka alkalan kotun tsarin mulki takwas sun goyi bayan kudurin da majalisar kasar da suka bayar da ya sami goyon bayan sama da kashi biyu cikin uku da ake bukata na goyon bayan tsige Park daga mukaminta.

An dauki wannan mataki ne biyo bayan zargin cin hanci da rashawa da kuma barin wata kawarta ta kud-da-kud ta rika shigar harkokin mulkin kasar, mu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG