Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tuhumi Pervez Musharaff Da Sanadin Kashe Benazir Bhutto


Musharaff

Wata kotu a kasar Pakistan ta tuhumi tsohon shugaban kasar Pervez Musharaf dangane da kisan gillan shugabar jam’iyar hamayyar kuma tsohuwar Firai Ministar kasar Benazir Bhutto.

Wata kotu a kasar Pakistan ta tuhumi tsohon shugaban kasar Pervez Musharaf dangane da kisan gillan shugabar jam’iyar hamayyar kuma tsohuwar Firai Ministar kasar Benazir Bhutto.

Kotun dake da zama a Rawalpindi ta tuhumi Mr. Musharraf yau Talata da kisan kai, da hada baki da kuma taimakawa wajen aikata kisan. Masu shigar da kara sun ce Mr. Musharraf, wanda shine shugaban kasa a lokacin, ya kasa kare Ms. Bhutto daga harin a wajen wani gangamin siyasa a Rawalpindi inda ta mutu bayan harbi da kuma harin bom da aka kai mata.
Mr. Musharraf ya musanta zargin da ake yi masa aka kuma dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan nan na Agusta.

Wannan ne karon farko a tarihin kasar Pakistan da ake tuhumar babban jami’in soja da aikata laifi. An dauki kwararan matakan tsaro a ciki da kewayen kotun yau Talata.

Mr. Musharraf ya koma Pakistan farkon shekarar nan bayan da ya sauka daga karagar mulki bayan an kunyatar da shi a shekara ta dubu biyu da takwas, ya kuma shafe kusan shekaru hudu yana gudun hijira na radin kansa. Ya lashi takobin tsayawa takara bayan komawarshi, sai dai aka haramta mashi shiga zabukan majalisa, yanzu kuma yana fama da tuhume-tuhume da dama.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG