Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Najeriya Ta Biya Diyyar Dala Biliyan 3.3 Ga Jihohin Ribas, Akwa-Ibom


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Wata babbar kotun tarayya da ke da zamanta a Abuja ta ba gwamnatin Najeriya wa’adin kwanaki 14 ta biya diyyar sama da dala biliyan 3 ga jihohin Ribas da Akwa-Ibom a matsayin wani bangare na kason kudaden shigar su daga cinikin danyen mai a kasuwannin duniya.

A yayin da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, mai shari’a Taiwo Taiwo ya umarci gwamnatin Najeriya ta biya wannan kudin cikin wa’adin kwanaki 14, tare kuma da biyan kudin ruwa kashi 8 cikin 100 a duk shekara, idan ta kasa biya a cikin wa'adin.

Kotun ta ce wannan kudin na matsayin wani kaso ne daga cikin dala biliyan 62 da rahotanni suka yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya Najeriya ta kwato daga wasu kamfanonin mai kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A yayin zartar da hukuncin, mai shari’a Taiwo Taiwo, ya ce batun fitar da sanarwar kare kai da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi ta baiwa jihohin da suka shigar da kara wato Ribas da Akwa-Ibom, kuskure ne daga bangaren gwamnatin kasar lamarin da ya ce ya sabawa doka.

Kotun ta kuma yi watsi da ikrarin gwamnatin Najeriya da ke cewa , ba zata iya biyan jihohin biyu kudadden shiga da ta samu daga cinikin danyen mai a kasuwannin duniya ba inda ta kara da cewa, kamata yayi gwamnati da a ke kara ta gabatar da hujojjin kare matsayinta kan kudadden shiga da ta samu a bangaren cinikin danyen mai kamar yadda doka ta tanada.

Wannan hukuncin babban kotun tarayyar na zuwa ne sa’o’i 24 bayan ita kotun ta umarci kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC da kamfanin Mobil da su biya zunzurutun kudi da ya kai naira biliyan 82 a matsayin diyya ga al’umman Ibeno da ke jihar Akwa-Ibom don illolin da malalar danyen mai ya haifar ga mutanen yankin.

Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya ce kamfanin man mallakin kasar Amurka da kamfanin NNPC, sun yi sakaci a yadda suka kula da matsalar malalar mai wanda ya haifar da gurbacewar muhalli a tsakanin al’ummomin yankunan da ya sanya cikin yanayim rayuwa mai tsanani.

XS
SM
MD
LG