Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Wanke Tsohon Manajan NNPC, Andrew Yakubu Kan Zargin Almundahanar Kudade


Tsohon Shugaban Kamfanin NNPC Mr.Andrew Yakubu

Babbar kotun taraiya ta wanke tsohon shugaban kamfanin NNPC Mr.Andrew Yakubu bisa zargin badakalar dala miliyan 9.8.

A shekarar 2017, Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Ƙasa EFCC ta kai samame wani gidan Yakubun da ke Sabon Tasha a Kaduna inda tae ta gano dala miliyan 9.7 da fam 74,000 a cikin wani ma’aji

Daga nan EFCC ta shigar da karar cewa Yakubu ya samu kudin ne ta hanyar da ba ta dace ba kuma kudin ba su bi ta banki ba.

Kotu
Kotu

Andrew Yakubu ya shaidawa kotu cewa kudin sun taru ne daga kyaututtukan da ya samu daga abokan sa bayan ajiye aiki a 2014.

Yakubu ya ce ya tara kudin ne a waje daya da kadan-kadan ba wai a dunkule ya same su ba.

Mai shari’a Ahmed Muhammed ya yanke hukuncin wanke Yakubu da umurnin a mayar ma sa kudin sa don kotu ta gamsu da hujjojjin da Yakubu ya gabatar.

Kotun ta ce EFCC ta gaza bincika gaskiyar an tara kudin ne da kadan-kadan kuma ba ta taba kawo kudin gaban kotun ba tun fara shari’ar.

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG