Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Abdulrasheed Maina Hukuncin Shekara 8 A Gidan Yari


Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina

Alkali Abang ya ce albashi da sauran alawus-alawus din Maina bai isa ya kai ga tara wadannan kudade ba.

Wata kotu a Abuja ta samu tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin biyan kudaden fansho da aka rusa Abdulrasheeh Maina da laifin halalta kudaden haram.

Alkali Okon Abang da ke sauraren shari’ar a kotun ta tarayya ya yanke mai hukuncin zaman gidan na tsawon shekara 8 a gidan yari kamar yadda rahotannin suka nuna.

Katun ta samu Maina da laifi a dukkan tuhume-tuhume 12 da aka yi masa a shari’ar.

Hukuncin da aka yankewa Maina na zuwa ne makonni bayan da aka yankewa dansa Faisal Abdurlrasheed Maina hukuncin zaman gidan bayan da shi ma aka same shi da laifin halalta kudaden haram da yawansu ya kai naira miliyan 58.

Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan da aka sami shi Mainan da handame naira biliyan 2 na masu karbar kudaden fansho a Najeriya.

An kuma same shi da laifin boye asalin sunansa da bayanansa a lokacin da ya je bude wasu asusu a wasu bankuna biyu.

Bayanai sun yi nuni da cewa Maina ya yi amfani da sunayen wasu iyalansa wajen bude asusan.

Faisal Maina
Faisal Maina

A cikin asusan biyu, an samu tsabar kudi naira miliyan 300 da miliyan 500 da kuma biliyan 1.5 kamar yadda kotun ta bayyana, inda ta ce Maina ya gaza ba da hujjar da za ta nuna cewa kudaden na halal ne.

Har ila yau Alkali Abang ya ce albashi da sauran alawus-alawus din Maina bai isa ya kai ga tara wadannan kudade ba.

Baya ga haka an same shi da laifin saba ka’ida wajen mallaka gida a Abuja wanda ya saya da tsabar kudi dala miliyan 1.4 ba tare da ya bi tsarin da hukuma ta tanada ba.

Wannan adadin kudi a cewar kotun, ya haura ka’ida da aka tanada ta sayen gida da kudinsa ya haura miliyan 5 ba tare da an sanar da hukuma ba.

XS
SM
MD
LG