Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Evans Hukuncin Daurin Rai Da Rai


Chukwudimeme Onwuamadike
Chukwudimeme Onwuamadike

Wani alkalin babbar kotun jihar lagos, Hakeem Oshodi ya zartar da hukuncin daurin rai da rai akan gawurtaccen mai garkuwa da mutanen nan na birnin Lagos  Chukwudimeme Onwuamadike da akafi sani da suna Evans.

Haka suma wasu masu mara masa baya su biyu – Uche Amadi and Okwuchukwu Nwachukwu an yanke masu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Kotun dai ta samu Evans da mutanen uku da hannu wajen sacewa da kuma garkuwa da Mr Donatius Dunu, mai kanfanin saida magungunan Maydon Pharmaceuticals Ltd.

A hukuncin da Alkali Hakeem Oshodi ya karanta masu dukkan mutanen uku bisa shedun dake gaban sa, kotun ta same su da laifin hada baki da kuma garkuwa da wannan dan kasuwa.

Sai dai alkali Oshodi ya bada umarnin a saki wasu mutanen hudu da ake tuhumar su tare bisa rashin sheda. Mutanen sun hada da Ogechi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi, wani tsohon soja da Victor Aduba, shima tsohon Soja.

An dai shafe shekaru kusan biyar ana wannan Shari'a, kuma Babban jami'in 'yan sanda Abba kyari da shima yanzu haka yake tsare bisa zargin mu'amala da masu safaran muggan kwayoyi ne ya kama Evans da mutanen nasa a legas.

XS
SM
MD
LG