Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Soke Zaben Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf


Engr. Abba Kabir Yusuf
Engr. Abba Kabir Yusuf

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

A zaman yanke hukuncin da aka yi ranar Juma'a 17 ga watan Nuwamba, kotun ta ayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Dama a baya Kotun sauraren kararrakin zabe ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ta bayyana cewa akwai kuru’u marasa inganci da yawa da aka kada wa Abba Yusuf.

A watan Satumba ne Yusuf ya kalubalanci hukuncin Kotun sauraron kararrakin zaben da ta soke nasarar da ya samu, inda ya daukaka kara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG