Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Fara Zaman Hukunta Charles Taylor


Tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor ya sadda kai ya na sauraren shari'ar da ake yi mi shi

Taylor ya ce kotun ta same shi da laifi ba tare da cikakkiyar fahimtar gaskiyar al’amarin ba

Tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor ya kare kan shi a gaban kotun Majalisar Dinkin Duniya, a daidai lokacin da alkalai suka saurari hujjoji a sharia’r hukunta shi saboda manyan laifuffukan yakin da aka same shi da aikatawa.

Taylor ya ce kotun mai cibiya a birnin Hague, ta same shi da aikata dukannin laifuffuka 11 da su ka hada da ta’addanci da kisa da kuma fyade a watan jiya ba tare da cikakkiyar fahimtar gaskiyar al’amarin ba.

Haka kuma ya zargi masu shigar da kara da biyan wadanda suka bada shaida game da shi haka kuma ya zargi kotun da hannu a wani makircin kasashen yamma game da shi da kuma sauran bakaken Afirka.

Lauyoyin Taylor sun yi watsi da bukatar masu shigar da kara, ta neman a yanke mi shi hukuncin daurin shekaru 80 a wani gidamn kason kasar Birtaniya, lauyoyin shi suka ce hukuncin ya yi matukar tsanani kuma su ka ce sun dorawa Taylor abubuwan keta da azabtarwar da suka faru a zamanin yakin kasar Saliyo.

Masu shigar da kara sun ce Taylor ne ya kitsa yakin basasar kasar Saliyo a shekarun 1990, kuma ya rika bada makamai da taimakawa ‘yan tawaye musanyar lu’ulu’un yaki da ake haka a gabashin kasar Saliyo.

Kotun ta gano cewa ba Taylor ba ne kwamandan 'yan tawayen kuma ba shi da iko da su amma ya na sane da abubuwan da suka aikata kuma ya taimaka mu su da makamai da sauran abubuwan da suke bukata.

Ranar 30 ga watan Mayu za a fadi irin hukuncin da za a yi mi shi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG