Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Wanke Gbagbo Amma ...


Tsohon Shugaba Laurent Gbagbo

Duk da yake kotun shari'ar manyan laifuka ta kasa da kasa ta wanke tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo daga zargin aikata laifin cin zarafin bil'adana, da sauran rina a kaba saboda masu gabatar da kara sun ce za su daukaka kara.

Masu gabatar da kara a kotun manyan laifuka ta kasa da kasa, sun ce za su daukaka kara saboda wanke tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo da aka yi daga laifin cin zarafin bil’adama, game da munanan tashe-tashen hankulan da su ka biyo bayan faduwarsa zaben shugaban kasa a 2010.

Kwamitin alkalai uku ya bayar da umurnin a saki Gbagbo da hadiminsa kuma tsohon Ministan Matasa na kasar Charles Ble Goude ba tare da bata lokaci ba, to amma an jinkirta aiwatar da umurnin zuwa yau Laraba saboda a bai wa masu gabatar da kara cikakken lokacin daukaka kara.

A martaninsu ga kotun, masu gabatar da karar sun bukaci da alkalan su gindaya tsauraran sharudda game da sakin na Gbagbo da Goude, su na masu nuni da yiwuwar su gudu idan su ka ga an yi nasara a daukaka karar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG