Accessibility links

Kotun ICC zata tuhumi shugaban mayakan Jamhuriyar Kwango da sababbin laifuka


Yan gudun hijira a kudancin Kwango

Babban mai shigar da kara na kotun bin kadin manyan laifukan yaki yana shirin tuhumar Bosco Ntaganda da wasu laifukan yaki.

Babban mai shigar da kara na kotun bin kadin manyan laifukan yaki yace yana shirin tuhumar shugaban kungiyar mayakan damokaradiyar jamhuriyar Kwango da wadansu karin laifukan yaki.

Tun shekara ta dubu biyu da shida kotun dake zama a birnin Hague take neman Bosco Ntaganda da ake yiwa lakabi da “terminator”, bisa laifin daukar kananan yara soja a yankin Ituri.

Babban mai shigar da kara Luis Moreno-Ocampo ya shaidawa manema labarai jiya Litinin a birnin New York cewa, yana so ya kara yawan laifukan da ake tuhumar Ntaganda da aikatawa da suka hada da gallazawa bil’adama akuba da kai harin kasa da kasa kan farin kaya.

Ntaganda wanda yake buya, ya jagoranci kungiyar ‘yan tawaye ta National Congress for the Defence of the People (CNDP). Sabon fadan da ya sake barkewa tsakanin sojoji da ‘yan tawayen dake karkashin jagorancin Ntagand a karshen watan Aprilu.

Moreno-Ocampo ya kuma sanar da neman takardar sammaci kan wani shugaban mayaka. Sylvestre Mudacumara, sabili da tashin hankalin da ya barke a lardunan Kivu ta kudu da kuma arewa. Mudacumara shine kwamandan kungiyar ‘yan tawayen Kwango, FDLR ko kuma Democratic Foreces for the Liberation of Rwanda

A wata sabuwa kuma, jiya Litinin ministan watsa labarai na kasar Kwango yace, “kasashen waje” suna iza wutar rikici a cikin kasarshi.

Lambert Mende ya shaidawa Muryar Amurka cewa, wadannan mutanen suna neman ganin ana ci gaba da tashin hankali a kasar, sai dai babu dalilin tunanin cewa, makwabtan damokaradiyar jamhuriyar Kwango suna da hannu a ciki.

XS
SM
MD
LG