Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kasa da Kasa Tayi Watsi Da Wanke Tsohon Mukaddashin Firayim Ministan Serbia


 Vojislav Seselj mai tsananin kishin kasa wanda ya ki yin nadama
Vojislav Seselj mai tsananin kishin kasa wanda ya ki yin nadama

Volislav Saselj tsohon mukaddashin firayim ministan Serbia bai tsira ba saboda kotun kasa da kasa ta tabbatar da hukumcin dauri da aka yi masa

Babban kotun kasa-da-kasa ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, dake duba laifukan yaki tayi watsi da hukuncin wanke tsohon mukaddashin Firayim Ministan Serbia Volislav Seselj, a 2016. Yanzu kotun ta daure shi shekaru 10.

Alkalan kotun daukaka kara dake Hugue sun yi anfani da jawabin da yayi a shekarar 1992 na sukar 'yan Croatia na cewa a kori 'yan Croatia a hukuntasu a zaman cin zarafin Bi’l Adama, saboda haka ne suka yi watsi da hukuncin da da ya wanke shi.

Sai dai kuma akwai yiyuwar Seselj zai iya ci gaba da zama mutun mai cikakken ’yanci domin ko ya riga ya kwashe shekaru 12 a gidan yari, tun bayan da ya mika kansa ga kotun kasa da kasa a shekarar 2003.

An dai sake shi ne a shekarar 2014 domin yaje ya nemi maganin cutar daji(CANCER), amma kuma ya ci gaba da zama dan majilisar dokokin kasar ta Serbia.

Sai dai Seselj yace hukuncin da alkalin ya yanke na baya-bayan nan ya sabawa doka kuma wannan bai sa yayi nadama ba akan wannan danyen aikin da aka tuhumeshi da aikatawa.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG