Wakilin Muryar Amurka a can Ghana, Baba Yakubu Makeri ya rawaito cewa kotun tayi amfani da minti 3 kacal, wajen yanke hukunci.
Alkalai 9 ne suka yanke wannan hukunci a karkashin shugabancin babban alkali Justice William Atuguba. Alkalin yace sauran alkalai sun bada ra’ayoyinsu, kuma aka tattarasu domin yanke hukunci.
Jami’iyyar ta shigar da karar yawan kuri’u, da kuma takardun kuri’u wadanda ba’a saka wa hannu. A cikin karar, harda rashin samun daman jefa kuri’u a wasu wuraren, amma kotun
Hukuncin da aka yanke shine na yin watsi da karar da babbar jam’iyyar adawa ta shigar, saboda haka shugaba John Dramani zai cigaba da jan ragamar kasar Ghana.