Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar APM, Ta Jingine Karar Atiku Da Jam’iyyar Labour Don Nazari


Babbar kotun tarayya
Babbar kotun tarayya

Kotun kolin mai mambobi bakwai da ke samun jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ne ta yanke wannan hukuncin a ranar Litinin jim kadan bayan da lauyoyin jam’iyyun da suka daukaka kara da wadanda ake kara suka amince daya-bayan daya da bayanansu.

Kotun koli ta yi watsi da karar jam’iyyar APM a bisa bukatar jam’iyyar tare da jingine karar da Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP da Labour suka shigar kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben watan Febrairun don yin nazari kafin ta yi zaman zartar da hukunci nan gaba.

Kotun kolin ta kuma saurari muhawara daga lauyoyi zuwa ga jam’iyyu kan bukatar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar na kawo sabbin shaidu kan takardun da ake zargin na jabu ne da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa hukumar INEC a yayin mika takardun neman takara.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Lauyan Atiku Abubakar, Mista Chris Uche, ya bukaci kotun da ta amince da bukatarsu kuma ta ba da damar daukaka kara, ta amince da dukkan bukatun da suke nema, sannan ta soke takarar shugaba Tinubu.

Tuni dai 'yan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da abin da suke sa ran zai wakana a kotun koli inda mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Muhammad Baloni ya bayyana cewa, duk abin da ya kasance a kotun koli, Najeriya ita ce kasarsu kuma yana fatan gwamnatin dake kań mulki za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da tsaro, abinci, da saura ababen more rayuwa.

Dakta Yunusa Tanko, jigo ne a jam’iyyar Labour, daya daga cikin jam’iyyu uku da suka daukaka kara a gaban kotun koli kuma ya bayyana cewa ya ji dadin yadda kotun koli ta karbi bayanan da jam’iyyarsa ta gabatar.

Ko mene ne jingine zaman sauraron karar da Atiku Abubakar, jam’iyyun PDP da Labour suka shigar ke nufi, babban lauya mai mukamin SAN, Magaji Garba ya ce, kotu ta saurari jawaban dukkan bangarorin da abin ya shafa, za ta yi nazari don zartar da hukunci nan gaba.

Idan Ana iya tunawa, a ranar 6 ga watan Satumbar shekarar 2023 ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben watan Fabrairun da hukuncin da ta zartar kuma jam’iyyun da ba su gamsu da abin da ya wakana ba suka daukaka kara a kotun kolin Najeriya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG