Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Kotunan Sauraren Kararrakin Zaben 2023 Na Ci Gaba Da Yanke Hukunci


ABUJA: Taron majalisun tarayyar Najeriya
ABUJA: Taron majalisun tarayyar Najeriya

Yayin da wasu ‘yan Majalisar Dokokin Najeriya ke rasa kujerun su a zauren kotunan sauraron kararrakin zabe a jihohi dabam daban na kasar, masana kimiyyar siyasa sun bayyana dalilan da ke sa wasu ‘yan siyasar ke faduwa zabe a gaban kotu.

Bayan shafe makonni ko watanni da dama ana fafata shari’a a gaban kotunan sauraron zabe tun bayan kammala zabuka a watannin Fabrairu da Maris, yanzu haka alkalan kotunan na fitar da hukunce-hukuncen shari’un, la’akari da yadda lokacin da doka ta shata musu ya dauko gangara.

A jihar Kano, jam’iyyar NNPP mai rike da gwamnati ta yi rashin kujerun Majalisar Wakilai guda uku, biyu daga ciki saboda matsalar takardun kammala makaranta, yayin da guda kuma saboda rashin aje aiki bisa tanadin doka kafin shiga zabe, a don haka kotun ta umarci hukumar zabe ta ba da shaidar cin zabe ga ‘yayan jam’iyyar APC.

Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso daga Mazabar Kura, Madobi-Garun Malam, daya daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar APC da suka samu nasarar a kotu, ya yi godiya ga Allah.

“Idan Allay ya sa na kama aiki zanyi da duk abin da ya kamata domin ganin cewa an kawo kayayyakin noma na zamani domin amfanin al’umar da nake wakilta, la’akari da cewa yankin da na fito na hada-hadar noman rani da damina kuma wannan batu na bunkasa harkokin noma na cikin abubuwan da mai girma shugaban kasa ya sanya a gaba."

Sai dai Alhaji Sanusi Sirajo Kwankwaso, da ke zaman mai bai wa gwamnan Kano shawara a kan harkokin siyasa ya ce za su daukaka kara.

“Ina karfafa giwar magoya baya da su kwantar da hankalinsu, wannan kotu ta yi abin da take ganin shine daidai, amma na yi amanna cewa kotu ta gaba zata dawo mana da kujerunmu,” a cewar Sirajo.

A jihar Sokoto kuma kotun kararrakin zaben ta kwace kujerar Majalisar Dokoki ta jihar daga hannun PDP zuwa APC saboda matsalar takardun karatu, yayin da a jihar Katsina PDP ta rasa ‘yan Majalisar Wakilai guda biyu, duka bisa dalilin wannan batu na kuskuren takaradar makaranta.

Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa malamin kimiyyar siyasa ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce babu mamaki rashawa da cin hanci da tsubbace-tsubbace a tsakanin wasu ‘yan siyasar da kuma zafafa bukatar mulki a zuci na daga cikin wasu daga cikin dalilan da kan sanya ‘yan siyasa su rufe ido su rinka aikata wadannan abubuwa.

Wannan batu na amfani da takardun bogi ko karya dokokin kasa yayin shiga zabe na cikin abubuwan da ‘yan takarar shugabancin Najeriya na PDP da LP, wato Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi suke kalubalantar zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu da su.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Najeriya: Kotunan Sauraren Kararrakin Zaben 2023 Na Ci Gaba Da Yanke Hukunci
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG