Accessibility links

Kotun kolin Astralia ta amince da hana talla kan kwalin taba sigari


Taba Sigari
Kotun kolin kasar Australia tace hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na cewa daga yanzu za’a rinka sayarda taba sigari a cikin kwalayen da basa da wani rubuce-rubuce ko hotunan janyo ra’ayi, bai saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba. A yau ne kotun kolin ta fito da wannan hukuncin, inda tayi watsi da karar da wasu kamfunnan taba sigari hudu suka shigar na cewa wannan kudurin na hana su saka rubuce-rubuce da hotunan ya taka musu hakkinsu. Saboda haka, daga watan Disambar wannan shekara, duk kwalayen taba sigari a kasar Australia zasu kasance iri daya ne – kuma zasu kasance kwalaye ne da abinda yake kansu sai hotuna da zane-zanen hukuma dake firgitarwa gameda shan taba sigari, inda za’a rinka nuna cutar shan tabar da hotunan yadda take bata lafiyar jikin mai shanta. Gwamnati na fatar cewa wannan matakin zai sa a sami raguwar mashaya taba a Australia inda kowace shekara, a lalace, taba shigari ta kan hallaka mutane 15,000.
XS
SM
MD
LG