Accessibility links

Kotun Phillipines Ta Bada Sammacin Kan Tsohuwar Shugabar Kasar Arroyo

  • Aliyu Imam

Tsohuwar shugabar kasar Philipines Arroyo daga hanun hagu.

Wata kotu a kasar Phillipines ta bada sammacin a kama tsohuwar shugabar kasar Gloria Arroyo kan zargin magudin zabe.

Wata kotu a kasar Phillipines ta bada sammacin a kama tsohuwar shugabar kasar Gloria Arroyo kan zargin magudin zabe.

Kotun ta dauki wan nan matakin ne bayanda hukumar zaben kasar ta amince da a gabatar da tuhuma kan tsohuwar shugabar kasar. Hukumar tace hukunci mafi tsanani idan aka sameta da aikata wan nan laifi shine daurin rai-rai.

Sommacin ya hana Madam Arroyo barin kasar. Ranar Talata Mrs Arroyo da maigidanta sunyi kokarin barin kasar cewa zata je neman jinya, amma aka dakatar da ita a tashar jiragen sama na Manilla.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG